28 Faburairu 2026 - 10:07
Source: ABNA24
An Ji Fashewar Abubuwa 3 A Tsakiyar Birnin Tehran + Hotuna

'Yan mintuna da suka gabata, an ji karar fashewar abubuwa uku masu karfi a tsakiyar birnin Tehran kuma an ga hayaki mai kauri ya tashi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa:  'yan mintuna da suka gabata, an ji karar fashewar abubuwa uku masu karfi a tsakiyar birnin Tehran kuma an ga hayaki mai kauri.

Yanzu, hayaki mai kauri ya na ci gaba da tashi daga kewayen Pasteur. Majiyoyin Ibrananci sun yi ikirarin cewa Isra'ila ta kai hari kan Iran.

Rahotanni na farko sun nuna cewa wasu makamai masu linzami sun afkawa titin Daneshgah da yankin Jomhuri.

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha